Sanarwar bayan taron kawo zaman lafiya a Siriya da aka yi a Rasha

A yayin taron tattauna wa kan sulhunta rikicin Siriya da aka gudanar a birnin Sochi na kasar Rasha an bukaci da a girmama 'yanci tare da martabar kasar.

900405

A jawabin bayan taro da aka fitar an bayyana cewa, al'umar Siriya ne ya kamata su sama wa kansu makoma ta hanyar zabe.

Sanarwar ta kuma ce, lallai ne a yi amfani da hanyoyi na siyasa wajen warware rikicin Siriya. 

Haka zalika an kara da cewa, Sojojin Siriya tare da dakarun kasashen waje za su ci gaba da tsaren iyakokinta, kuma al'umar Siriya na da matsayi iri daya ba tare da duba da Addini, yare ko asali ba.

Mahalarta taron sun kuma ce, domin yi wa kundin tsarin mulkin Siriya na yanzu kwaskwarima za a kafa kwamiti mai mutum 150, kuma an amince kan a kawo karshen yakin da aka dauki shekaru 7 yi ana yi a kasar.Labarai masu alaka