Gidey ta kafa tarihi a gasar tsere ta mata ta duniya

'Yar kasar Itopiya Letesenbet Gidey ta kafa tarihi a gasar mata ta tseren mita dubu 10 ta duniya.

1655059
Gidey ta kafa tarihi a gasar tsere ta mata ta duniya

'Yar kasar Itopiya Letesenbet Gidey ta kafa tarihi a gasar mata ta tseren mita dubu 10 ta duniya.

Gidey ta yi gudun mita dubu 10 a mintuna 29.01.03 a wajen gasar Wasannn FBK da ake gudanarwa a garin Hangelo na kasar Holan wanda hakan ya sa ta kafa tarihi.

'Yar wasan mai shekaru 23 ta doke 'yar kasar Holan kuma 'yar asalin Itopiya Sifan Hassan wadda a ranar 6 ga Yuni ta yi nasarar zama na daya a gasar bayan yin gudun mita dubu 10 a cikin mintuna 29.06.82.

 Labarai masu alaka