Yazici ya karbi kambin zama Zakaran Dan Wasa na Faransa

An bayar da kambi ga dan wasan kwallon kafa dan kasar Turkiyya Yusuf Yazici wanda aka zaba a matsayin Zakaran Dan Wasan Kwallon Kafa na Faransa a watan da ya gabata.

1573134

Dan wasan mai shekaru 23 ya yada hotonsa tare da kambin a shafinsa na sada zumunta.

Ya ce "Ina matukar farin cikin zama Baturke na farko da ya samu kambin zama Zakaran Dan Wasa a Faransa. Ina godiya ga dukkan wadanda suka bayar da goyon baya."

A shafin yanar gizo n Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ne aka gabatar da sunayen Yusuf Yazici, Tino Kadewere da Karl Toko-Ekambi don a zabi daya daga ciki a matsayin Zakaran Dan Wasan Kasar.

 Labarai masu alaka