Real Madrid ta samu babbar dama

Kungiyar Real Madrid ta Spaniya ta samu babbar dama bayan jefa kwallo 1a minti na 45 ta kafar dan wasanta Casemiro a wasan da ta buga da kungiyar Espanyol.

1445677
Real Madrid ta samu babbar dama

Kungiyar Real Madrid ta Spaniya ta samu babbar dama bayan jefa kwallo 1a minti na 45 ta kafar dan wasanta casemiro a wasan da ta buga da kungiyar Espanyol, wadda ita ce ta karshe a gasar La Liga kuma wadda ta yi sauyin mai horar da 'yan wasanta a kwanaki 3 da suka gabata.

Real Madrid ta ji dadin yadda Barcelona ta yi kunnen doki 2 da 2 da Celta Vigo wanda hakan ya sanya ta dare kan gaba a gasar La Liga ta Spaniya.

A lokacinda ya rage makonni 6 a gama gasar Laliga, Real Madrid na da maki 71, Barcelona maki 69, Atletico Madrid 58, Sevilla na da maki 54 sai Espanyol kuma da ke da maki 24.

 

 



Labarai masu alaka