An dakatar da Besedin daga buga wasanni na tsawon shekara 1

Hukumar Kula da Wasannin kwallon Kafa ta Turai UEFA ta dakatar da dan wasan gaba na kungiyar Dinamo Kiev da ke Yukren, Artem Besedin daga buga wasanni na tsawon shekara daya sakamakon samun sa da ta'ammuli da kwayoyin kara kuzari.

1417226

Sanarwar da aka fitar ta shafin yanar gizon UEFA ta bayyana cewar a karshen wasan da Dinamo Kiev ta buga Malmo ta kasar Swidin ne aka gudanar da gwaji a kan 'yan wasa inda aka gano Artem Besedin ya yi amfani da maganin da aka haramtawa 'yan wasa sha, wanda hakan ya sanya aka dakatar da shi na tsawon shekara 1.

Bayan da dan wasan bai daukaka kara ba bayan fara binciken na nuni da hkuncin ya tabbata.

Dan wasan da Dinamo Kiev ta raina da kanta ya jefa kwallaye 2 a wasanni 12 da ya buga.Labarai masu alaka