An dage gasar Zakarun Turai har sai abunda hali ya yi

Sakamakon annobar Corona (Covid-19) Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kafa ta Turai UEFA ta sanar da dakatar da dukkan harkokin wasannin gasar Zakarun Turai har sai abunda hali ya yi.

1383847

An dage wasannin karshe na gasar Zakarun Turai ta maza, gasar Europa da  gasar kwallon kafa ta mata ta Turai da aka shirya yi a watan Mayu.

A jadawalin da aka fitar a farkon kakar wasannin Zakarun Turai an bayyana za a buda wasan karshe na gasar Zakarun Turai a ranar 30 ga watan Mayu a filin wasa na Ataturk Olympics dake Istanbul, wasan karshe na gasar Europa kuma za a buga a ranar 27 ga Mayu a filin wasa na Gdansk dake Polan, gasar mata kuma za a buga a ranar 24 ga watan Mayu a filin wasa na Viola Park dake Ostiriya.

Shugaban EUFA Aleksander Ceferin ne zai jagoranci sanar da sabon lokacin da za a buga wasannin a nan gaba.Labarai masu alaka