Tsohon shugaban hukumar kwallon kwandon Amurka ya mutu

An sanar da mutuwar tsohon shugaban hukumar kwallon kwandon kasar Amurka David Stern yanada shekaru 77

1333419
Tsohon shugaban hukumar kwallon kwandon Amurka ya mutu

An sanar da mutuwar tsohon shugaban hukumar kwallon kwandon kasar Amurka David Stern yanada shekaru 77.

Hukumar kwallon kwandon ta Amurka watau NBA ta sanar da cewa Stern wanda aka kwantar asibiti domin yi masa tiyata sanadiyar rubar jini a kwakwalwarsa ya riga mu gidan gaskiya.

Stern, ya kasance shugaban NBA tsakanin shekarar 1984-2014, ya jagoranci hukumar na tsawon shekaru 30 shugaba mafi dadewa da hukumar ta taba yi.

A lokacin da yake jagoran hukumar ya kawo sauye-sauye da bunkasar kungiyoyin wasan kwallon kwandao da kuma habaka wasan a fadin duniya.

 Labarai masu alaka