Dambele ya ji rauni

Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta bayyana cewa dan wasanta Ousmane Dambele ba zai buga wasanni ba har tsawon makwanni 10 sakamakon raunin da yaji alokacin wasa.

Dambele ya ji rauni

Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta bayyana cewa dan wasanta Ousmane Dambele ba zai buga wasanni ba har tsawon makwanni 10 sakamakon raunin da yaji alokacin wasa. 

Rahotanni sun nuna cewa dan wasan mai shekaru 22 ya ji raunin ne a wasi wasa da kulob din ya buga da kulob din Jamus na Dortmund a minti na 25.

A farkon kakar nan ma dai dan wasan ya ji rauni inda ya kwashe wata daya da rabi bai taka leda ba. 

A shekarar 2017 Dambele ya shigo kulob din inda Barcelona ta biya Euro miliyan 105 a matsayin kudin fansa.

Tag: Dambele

Labarai masu alaka