NBA ta haramta wa John Collins buga wasanni 25

Dan wasan kwallon kwandon Amurka John Collins mai buga wasa a kulob din Hawks na cikin matsala yayinda aka haramata masa buga wasanni 25 kan cewa ya yi anfani kwaye a lokacin wasa.

Wani bayani da aka yi daga Hukumar Kwallon Kwando ta NBA ya nuna cewa an gano cewa jikin dan wasan na dauke da wata kwaya mai suna Peptide-2 sakamakon wani gwaji da aka yi. 

Kamar haka ne dai dan wasan ba zai buga wasanni 25 masu zuwa ba sannan ba za a bashi albashi ba har sai ya dawo aiki. 

Dan wasan mai shekaru 22 ne dai dan wasa na uku da Hukumar FIFA ta hukunta a wannan kakar. 

Dan wasan Brooklyn Nets mai suna Wilson Chandler da kuma dan wasan Phoenix Suns mai suna Deandre Ayton na daga cikin wadanda aka hukunta a wannan kakar. Labarai masu alaka