Turkiyya ta ba wa Albeniya kashi a wasan zabe na EURO 2020

Turkiyya ta ba wa Albeniya kashi da ci 1 da 0 a wasan tantance kungiyoyin da za su shiga Gasar Cin Kofin Zakarun Turai na shekarar 2020 inda Turkiyya ke cigaba da fafatawa a runukin H.

Albeniya da Turkiyya sun fafata da juna har zuwa minti na 90 inda a nan ne Cenk Tosun ya zura kwallo daya a ragar Albeniya inda aka kammala wasan yayinda Turkiyya ta shige gaba da ci 1. 

Turkiyya ta lashe wasanni 6 cikin 7 da ta buga ila yanzu inda ta tara maki 18 inda ta shige gaban dukkan kasashe a rukunin H. 

Niyu Zilan na da maki 12 inda Albeniya ke biyo bayanta da maki 9 a rukuni na H. 

A ranar 14 ga watan Oktoba Turkiyya za ta fafata da Faransa inda Faransa na daya daga cikin manyan kasashe da ta gagari kowa a rukunin H. Labarai masu alaka