Yadda wasannin ƙwallon ƙafa zai kasance a Turkiyya wannan makon

An fitar lokutan wasannin ƙwallon ƙafa ta ƙasar Turkiyya wato Spor Toto Super League na mako karo na hudu.

Yadda wasannin ƙwallon ƙafa zai kasance a Turkiyya wannan makon

An fitar lokutan wasannin ƙwallon ƙafa ta ƙasar Turkiyya wato Spor Toto Super League na mako karo na hudu.

A yau dai da karfe 21.45 Evkur Yeni Malatyaspor ve da Atiker Konyaspor zasu barje gumi.

A gobe kuwa, da karfe 19.15 kungiyar kwallon ƙafar Fenerbahçe da Kayserispor ne zasu ja daga. A daidai wannan lokaci kuma Akhisarspor da Demir Group Sivasspor zasu gwada gwaninta.

Da karfe 21.45 Trabzonspor da Galatasaray ne zasu kara, sai kuma Aytemiz Alanyaspor da Goztepe a wannan lokacin.

A ranar Lahadi biyu ga watan Satumba, da karfe 19.15 Büyükşehir Belediyesi Erzurumspor da Medipol Başakşehir zasu ja daga

Da ƙarfe 19.15 Kasımpaşa ne zasu barje gumi da Ankara gücü.

Da 21.45 kuwa Antalyaspor ce zata fafata da Çaykur Rizespor.

Da karfe 21.45 kuma Bursaspor da Basiktas zasu fafata.

 Labarai masu alaka