Gobe za a barje gumi a zango 16 na gasar cin kofin duniya

Hankalin milyoyin ma'abota kwallon kafa ya karkata ga wasannin zango na 16 na gasar cin kofin duniya,wadanda za a buga gobe.

1002979
Gobe za a barje gumi a  zango 16 na gasar cin kofin duniya

Hankalin milyoyin ma'abota kwallon kafa ya karkata ga wasannin zango na 16 na gasar cin kofin duniya,wadanda za a buga gobe.

A ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2018, kungiyoyi kwallon kafa 4 ne zasu barje gumi.

Karawar farko za a yi ta ne a Moscow, babban birnin kasar Rasha a filin Luzhniki inda aka gudanar da shagulgulan share fage na gasar ta bana.

A karfe 17h00, mai masaukin baki, Rasha da Spain ne za su kara.

Wannan shi wasa ne biyu da Rasha za ta buga a filin Luzhniki.

A wasanta na Farko, ta lallasa Saudiyya da ci 5 da nema.

A karo na farko Spain za ta buga wasa a Moscow.

Spaniyawa sun buga wasanninsu 3 a filayen Sochi,Kazan da kuma Kaliningrad.

A karfi 21h00 na gobe kuma, Croatia mai maki 9 za ta kara Danmak a filin wasan Nizhny Novgorod,inda ta lallasa Argentina da ci 3 da nema.

 Labarai masu alaka