Kungiyar kasar Turkiyya ta taimakawa iyali 800 a Yemen

Kungiya mai zaman kanta ta kasar Turkiyya mai suna Sadaka Tasi ta baiwa iyali 800 da suka rasa matsugunansu tallafi a yankunan Taiz da Marib dake kasar Yemen

1596261
Kungiyar kasar Turkiyya ta taimakawa iyali 800 a Yemen

Kungiya mai zaman kanta ta kasar Turkiyya mai suna Sadaka Tasi ta baiwa iyali 800 da suka rasa matsugunansu tallafi a yankunan Taiz da Marib dake kasar Yemen.

Kungiyar ta bayyana cewa taimakon ya kunshi abinci, magani, abin sha da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

An bayyana cewa a cikin ko wani sakon 10 yaro daya na mutuwa sabili da yunwa a Yemen.

Shugaban kungiyar Kemal Ozdal ya bayyana cewa da yawan al’umman kasar Yemen na bukatar taimako sabili da yakin da kasar ke ciki.Labarai masu alaka