Corona ta yi ajalin karin mutane 64 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 64 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

1596379
Corona ta yi ajalin karin mutane 64 a Turkiyya

A awanni 24 da suka gabata mutane 64 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

Tun daga farkon bullar annobar zuwa yau, jimillar mutane dubu 28,965 ne suka mutu a kasar.

A rana guda an yi wa mutane 138,592 gwaji inda aka samu 11,770 na dauke da cutar, kuma 702 na da alamun rashin lafiya.

An kuma sallami karin mutane 7,291 wanda ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa miliyan 2 da dubu 616 da 139.

 Labarai masu alaka