Turkawa a fadin duniya na bukukuwan Ranar Kafa Jamhuriya

A cikin kasar Turkiyya, ofisoshin jakadancinta da ke waje da kuma Jamhuriyar Turkiya Arewacin Cyprus ana gudanar da bukukuwan ranar cika shekaru 97 da kafa Jamhuriya.

1517936
Turkawa a fadin duniya na bukukuwan Ranar Kafa Jamhuriya
5bd8387503d1d.jpg

A cikin kasar Turkiyya, ofisoshin jakadancinta da ke waje da kuma Jamhuriyar Turkiya Arewacin Cyprus ana gudanar da bukukuwan ranar cika shekaru 97 da kafa Jamhuriya.

A wani bangare na bukin, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Anitkabir. Erdogan da 'yan tawagarsa sun ajje furenni a hubbaren Ataturk.

Bayan kammala ziyartar Anitkabir an ci gaba da gudanar da bukukuwa a Fadar Shugaban Kasa. Shugaba Erdogan ya na ci gaba da karbar sakonnin taya murna. Ana sa ran Shugaba Erdogan zai kaddamar da nuna hotunan Gwagwarmayar Kasa sakamakon wannan rana ta musamman.

A Babban Birnin Turkiyya Ankara ana ci gaba da gudanar da bukin. Za a fara tattaki daga Majalisar Kasa ta Turkiyya zuwa ginin Majalisa ta Farko. Kafin tattakin, za a gudanar da babban buki.

An rufe wasu hanyoyi a Ankara sakamakon bukin ranar Jamhuriya.

Ba da iyakacin wannan buki kawai bukukuwan ranar Jamhuriyar za su tsaya ba.

Da misalin karfe 19.23 za a gudanar da casu a Tsohon Garin Tarihi Patara na Antalya, karkashin kulawar Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya.

Sannan za kuma a kunna nutso sau 97 a tekun Bahar Rum tare da yinw asan wuta.Labarai masu alaka