Corona ta yi ajalin fiye da mutum dubu 5 a Turkiyya

A kasar Turkiyya an bayyana cewa an samu mutuwar karin mutum 17 sanadiyar corona a cikin awanni 24

1444732
Corona ta yi ajalin fiye da mutum dubu 5 a Turkiyya

A kasar Turkiyya an bayyana cewa an samu mutuwar karin mutum 17 sanadiyar corona a cikin awanni 24.

Tun farkon annobar kawo yanzu mutum dubu 5 da 82 suka rasa rayukansu.

A jiya an yiwa mutane dubu 45 da dari 213 gwajin kwayar cutar inda aka samu dubu daya da dari 372 dauke da ita.

A jiyan an sallamai mutum dubu 1 da dari 984 a jumlace mutum dubu 169 da dari 182 sun warke daga cutar a kasar.

 Labarai masu alaka