Rukunai da Ka’idojin Tsaron kasar Turkiyya

Bayan yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli shekarar 2016, karkashin jagorancin shugaba Recep Tayyip Erdoğan, Turkiyya ta kaddamar da sabbin ka’idojin tsaron kasa

1425651
Rukunai da Ka’idojin Tsaron kasar Turkiyya

Bayan yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli shekarar 2016, karkashin jagorancin shugaba Recep Tayyip Erdoğan, Turkiyya ta kaddamar da sabbin ka’idojin tsaron kasa. Domin kare kasar Turkiyya daga dukkanin kalubale da nisanta ta daga ko wani irin barazana; an dauki matakai a iyakokin kasar da kuma yin hadin gwiwar soji da kasashe da dama ta hanyar kafa sansanoni. Hakika baya ga hanyar diflomasiyya an kuma bi hanyar soja domin samawa yankin baki daya tsaro mai inganci. Turkiyya sakamakon karfafa kanfunan tsaron kasarta da ta yi, ta samawa sojojinta dukkanin abubuwan da suke bukata; ta kuma kasance muhimmiya a fagen fitar da kayayyakin tsaro zuwa kasashen waje.

Akan wannan maudu’in mun kasance tare da Mal. Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA…

Lamurkan tsaron kasar Turkiyya da ma tsaron yankin sun sauya musamman bayan yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli. Sanadiyar hakan Turkiyya ta kaddamar da wasu ka’idojin da suka sanya kara karfin gwiwar yakar kungiyoyin ta’addancin PKK da DEASH, samar da daidato a Siriya da kuma nisanta kanta daga dukkanin nau’ukan barazana. Akan hakan ne bayan yunkurin juyin mülkin ta kaddamar da Farmakin Garkuwar Firat inda ta fatattaki ‘yan ta’addar DEASH da PKK daga Azeez zuwa kudancin Jerablus har izuwa garin Bab dake Siriya.

Karkashin yaki da kungiyar ta’addar DEASH Turkiyya ta ga cewa kasar Amurka na yunkurin kafa gwamnatin ta’addanci a yankin lamarin da ya sanya ta fara daukar kwararar matakai domin kange hakan. Bayan Farmakin Garkuwar Firat, ta kuma kaddamar da Farmakin Reshen Zaitun a Afrin da kuma Farmakan Shirin Zaman Lafiya a yankunan Tel Abyad da Resulayn domin kakkabe ta’addanci. A wadannan farmakan baya ga rundunar sojin Turkiyya sojojin Siriya masu zaman kansu ma sun halarta. Haka kuma, Turkiyya ta kwantar da hankalin al’umma da kange kwararar ‘yan gudun hijira sabili da kaddamar da Farmakin Garkuwar Bazara a yankin Idlib. Turkiyya dai na cigaba da ayyanar da farmakai a arewacin Iraki da sauran iyakokinta. Da ire-iren wadannan farmakan ne Turkiyya ta ke kauda kungiyar ta’addar PKK daga yankunan. Haka kuma da taimakon jami’an leken asirin Turkiyya anka yi nasarar magance jagororin  kuniyar ta’addar PKK a yankunan Siriya-Iraki. A yayin kaddamar da dukkanin wadannan farmakan Turkiyya ta yi amfani da jiragen yaki marasa matuka na cikin gida da kuma wasu makaman tsaron sararin samaniya da na kasa wadanda aka yi a cikin kasar. Hakan wani muhimmin sauyi ne a harkokin kariya ga rundunar sojan Turkiyya.

A yayinda Turkiyya ke fatattakar ‘yan ta’adda a sassan Iraki-Siriya tana kuma yin hadaka da rundunar sojin gwamnatin Libiya domin karfafa su a kasar. A Katar ma ta kafa sansani, a Somaliya kuma tana kaddamar da wasu tsarukan sauyi domin gudanar da ayyukan hukuma bisa wasu tsarukan. Ka’idoji da sabbin tsarukan Turkiyya basu kasance na diflomasiyya kawai ba, sun kuma kasance na daukar matakan soja, tare da kanfunan tsaron kasar ta kasance mai karfi da ke iya kera makaman amfanin kanta da kuma ma iya fitar dasu zuwa kasashen waje.

Wannan sharhin Mal. Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya…Labarai masu alaka