Bam mafi girma na Daular Usmaniyya

Ko kun san cewar a zamanin baya Daular Usmaniyya ce ta yi amfani da bam mafi girma a duniya a lokacin Fathu Istanbul?

1422072
Bam mafi girma na Daular Usmaniyya

Duk da har zuwa shekarar 1452 an yi amfani da bama-bamai a duniya amma babu wanda ya yi amfani da irin na Daular Usmaniyya. A lokacin da Jama’ar Usmaniyya suka zo bakin katangar Istanbul za su kame garin, jama’ar Bizans sun dinga kare bama-baman da ake jefa musu da garkuwa amma kuma sai su koma su yi wa katangar tasu barna.

Babban bam na Daular Usmaniyya a lokacin ya kai tsayin mita 8. na da fadin centimita 75 kuma yana da daukar kanana harasan wuta kilo 544. Ana kwashe awanni 3 kafin a cika shi, kuma a rana sau 6 kawai ake iya harba shi. Yana da nauyi sosai yadda wanda ya kera shi Urban na Hungary ya yi masa sassa 2. A wancan lokacin ana amfani da kusoshi wajen jona bangarorin 2. Sai da jama’ar Bizans kwararru suka dauki makonni 2 suna aikin gyaran katangar da bam din ya lalata.

An yi amfani da wannan bam shekaru 5-354 bayan Fathu Istanbul a shekarar 1807. A lokacinda Turawan Ingila suka yi yunkurin wucewa ta mashigar ruwan Canakkale, an harba shi wanda ya tilastawa jiragen ruwa ja da baya. Daga baya an kera irin sa don tunawa da bam din Sarki Abdulaziz kuma aka ba wa Ingilawa kyautarsa. Wannan kyauta na nan a ajje a gidan Adana Kayan Tarihi na Fort Nelson da ke Ingila.Labarai masu alaka