Corona ta yi ajalin karin mutane 23 a Turkiyya

Ana ci gaba da samun nasarar yaki da annobar Corona (Covid-19) a Turkiyya inda a kowacce rana adadin wadanda cutar ke kashewa yake raguwa.

1420863
Corona ta yi ajalin karin mutane 23 a Turkiyya

Ana ci gaba da samun nasarar yaki da annobar Corona (Covid-19) a Turkiyya inda a kowacce rana adadin wadanda cutar ke kashewa yake raguwa.

A ranar Larabar nan mutane 23 sun sake rasa rayukansu wanda ya kawo jimillar adadin wadanda cutar ta kashe a Turkiyya zuwa dubu 4,222.

A dai wannan lokaci an yi wa mutane dubu 20,838 gwaji inda aka samu dubu 1,022 dauke da Corona.

An kuma sallami karin mutane dubu 1,092 wanda ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa dubu 113,997.

 Labarai masu alaka