Corona ta yi ajalin karin mutane 28 a Turkiyya

Ana ci gaba da samun nasarar yaki da annobar Corona (Covid-19) a Turkiyya inda a kowacce rana adadin wadanda cutar ke kashewa yake raguwa.

1420199
Corona ta yi ajalin karin mutane 28 a Turkiyya

Ana ci gaba da samun nasarar yaki da annobar Corona (Covid-19) a Turkiyya inda a kowacce rana adadin wadanda cutar ke kashewa yake raguwa.

A ranar Talatar nan mutane 28 sun sake rasa rayukansu wanda ya kawo jimillar adadin wadanda cutar ta kashe a Turkiyya zuwa dubu 4,199.

A dai wannan lokaci an yi wa mutane dubu 25,382 gwaji inda aka samu dubu 1,022 dauke da Corona.

An kuma sallami karin mutane dubu 1,318 wanda ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa dubu 112,895.Labarai masu alaka