Wadanda cutar Corona ta yi ajali a Turkiyya sun karu zuwa mutane 59

Ya zuwa yanzu mutane 59 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

1385571
Wadanda cutar Corona ta yi ajali a Turkiyya sun karu zuwa mutane 59

Ya zuwa yanzu mutane 59 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19) a Turkiyya.

Ministan Lafiya Fahrettin Koca ta shafinsa na Twitter ya bayyana cewar "Marasa lafiyarmu 15 sun yi bankwana da rayuwa. Ya zuwa yau mu rasa mutane 59."

Minista Koca ya ce a wanni 24 da suka gabata an yi wa mutane dubu 5,035 gwaji inda aka samu mutane 561 dauke da Corona.

Bayan Ministan lafiyar ya kammala taro da Kwamitin Malaman Kimiyya ya gudanar da taron manema labarai inda ya ce an sallami mutane 26 da suka warke.

Ministan Ilimi na Turkiyya da ya halarci taron ya sanar da kara hutun makarantu har nan da 30 ga watan Afrilu amma dalibai za su ci gaba da daukar darasi daga gida ta yanar gizo.Labarai masu alaka