Turkiyya ta sayo magungunan cutar Corona daga China

Tun bayar bullar cutar Corona a Turkiyya ya zuwa yanzu adadin mutane 37 ne suka rasa rayukansu.

1384292
Turkiyya ta sayo magungunan cutar Corona daga China

Tun bayar bullar cutar Corona a Turkiyya ya zuwa yanzu adadin mutane 37 ne suka rasa rayukansu.

Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya fadi cewa "A cikin awanni 24 da suka gabata an yi wa mutane dubu 3,672 gwaji. An samu 293 dauke da cutar Corona. Duk da kokarin da ake yi wasu mutane 7 sun sake mutuwa daga cutar."

Minista Koca ya ka da cewar "Ba kwa cikin annobar. Ku tafiyar da rayuwarku a hankali. Kar ku shiga cikin hatsari. Kar ku kai hatsari gidajenku. Ku zauna a gida, rayuwa tana yiwuwa a gida."

Miistan na Lafiya ya kuma ce ya zuwa yanzu mutane 37 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Corona a Turkiyya daga cikin 529 da ta kama.

A gefe guda Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya ce sun kawo magungunan cutar ta Corona (Covid-19) daga China inda bayan sauke su a Ankara aka yi amfani da jiragen sama wajen kai su garuruwa 40 na kasar.

Minista Koca ya ce za a yi amfani da magunguna ga marasa lafiyar da suke dakin kula da wadanda ke cikin mawuyacin hali.

 
Labarai masu alaka