Turkiyya ta sake kashe sojojin Siriya 55

Turkiyya ta sake kashe sojojin Siriya 55 sakamakon hare-haren da ta kai musu a yankin Idlib.

Turkiyya ta sake kashe sojojin Siriya 55

Turkiyya ta sake kashe sojojin Siriya 55 sakamakon hare-haren da ta kai musu a yankin Idlib.

Ma'aikatar Tsaro ta Kasa ta Turkiyya ta sanar da cewa "Bayanan da aka samu daga majiyoyi da dama dake yankin Idlib sun tabbatar da an kashe sojojin gwamnatin Siriya 55."

A kwanakin baya ne sojojin Siriya suka kashe dakarun Turkiyya 5 a yankin Idlib da aka haramta rikici a cikinsa.

Sakamakon hakan Turkiyya ta sha alwashin mayar da martani ga Siriya.

 Labarai masu alaka