'Yan ta'adda na ci gaba da mika wuya ga jami'an tsaro a Turkiyya

A yayin da ake ci gaba da jawo hankalin 'yan ta'adda wasu mambobin kungiyar ta'addar PKK biyar sun mika wuya ga jami'an tsaro dake kofar Habur

'Yan ta'adda na ci gaba da mika wuya ga jami'an tsaro a Turkiyya

A yayin da ake ci gaba da jawo hankalin 'yan ta'adda wasu mambobin kungiyar ta'addar PKK biyar sun mika wuya ga jami'an tsaro dake kofar Habur.

Dangane da sanarwar da ta fito daga ma'aikatar harkokin cikin gidan Turkiyya sanadiyar matakan da jami'an tsaro sun ka dauka an fara samun nasarar akan magance matsalolin kungiyar ta'addar PKK\KCK.

An dai samu gagarumin nasara a shirin na fadakarwa wanda ake gudanarwa tare da goyon baya da hadin kan dangin mambobin 'yan ta'dda.

A wannan tsarin hukumomin tsaron yankin kofar Habur dake Sirnak sun yi nasarar shawo kan 'yan ta'adda biyar inda suka mika wuya.

A bisa wannan tsarin daga farkon shekara kawo yanzu 'yan ta'adda 13 sun tuba sun mika wuya ga jami'an tsaro.

 Labarai masu alaka