Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 20.01.2020

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 20.01.2020.

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 20.01.2020

Sabah: "Sanarwar Taron Libiya"

An fitar da sanarwa game da taron da aka gudanar a Berlin babban birnin Jamus, domin fara shirin tsagaita wuta na dindindin da samar da tsarin siyasa a Libiya. Sanarwar karshe ta yi kira ga bangarorin da magoya bayansu, da su tsagaita wuta tare da kawo karshen aiyukansu na soja tare da takunkumin amfani da makamai na Majalisar Dinkin Duniya (MDD).

Haber Turk: "Shugaban Turkiyya, Erdogan ya bayyanna cewa Mitsotakis yana wasa mara kyau"

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya mayar da martani ga Firaministan Girka, Kyriakos Mitsotakis wanda ya gayyata tare da tattauna da dan juyin mulki Janar Haftar Khalifa, wanda shi ne shugaban rundunar sojojin da ke da goyon bayan yakin basasa a Libiya. A taron NATO Erdogan ya tattauna da Mitsootakis, na tsawon awa 1 da rabi nda ya fada masa cewa goyon bayan Hafter da yake yi kuskure ne kuma hakan ba mataki ne mai kyau ba ga alakarsu da.

Yeni Safak: "Fitar da kudin tallafi na shekarar 2019 ya kafa tarihi"

Ministar Kasuwanci ta Turkiyya, Ruhsar Pekcan ta bayyana cewa shekarar 2019 ce ta zinari dangane da taimakon jihohi don fitar da kaya. Ta kara da cewa "Mun kafa tarihi a tarihin Jamhuriyar kan kasafin kudin tallafi kuma mun samu goyon bayan jihohi mafi wajen fitar da kayayyaki waje zuwa yau da lira biliyan 3.2. A cikin shekarar 2020, zamu gabatar da cikakken kasafin kudi na lira biliyan 3.8 don fitar da kaya da aiyuka.

Star: "Tarayyar Turai (EU): Ba za a yanke kudaden da ake ba wa Turkiyya ba"

Tarayyar Turai (EU) ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne ikirarin da ake na za a yanke tallafin kudi da ake ba wa Turkiyya. A ranar Lahadin nan ne kafafan yada labarai na Jamus suka fitar da labaran za a yanke kudin da ake ba wa Turkiyya da kaso 75 cikin dari.


Tag: Jaridu

Labarai masu alaka