Turkiyya ta yi wa Faransa raddi game da anfani da tsananin karfi

Turkiyya ta yi alla-wade da tsarin da Faransa ke bi wajen kawo karshen zanga-zangar dake gudana a kasar inda Turkiyya ta nuna rashin amincewarta da harin da aka kai wa dan jaridarta.

Turkiyya ta yi wa Faransa raddi game da anfani da tsananin karfi

Gwamnatin Ankara ta yi wa Faransa martani game harin da yan sandan Faransa suka kai wa masu yin zanga-zanga inda dan jaridan Turkiyya ya kasance yana wurin yayinda ya jikkata sakamakon hakan.

Kamar haka ne dai Shugaban Ofishin Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya yi jawabi ta shafinsa na twitter inda ya yi alla-wade da irin tsananin karfi da Jami'an tsaron Faransa ke anfani da shi.

Altun, ya yi jawabi kamar haka, 

"Ina matukar yin raddi da harin barkwanon tsohuwa da aka kai wa dan jaridan Turkiyya Mustafa Yalcin a birnin Paris".

A gefe guda Ofishin Harkokin Wajen Turkiyya ya ce, 

"Muna raddi da tsananin karfi da Faransa ke anfani da shi".

 

 Labarai masu alaka