Farmakan Tafkin Zaman Lafiya

Manufar ita ce zaman lafiya,
ta'addanci ake nufa

"Ba zamu fasa sayen S-400 daga Rasha ba"

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar Turkiyya bata fasa sayen makami ƙirar S-400 daga ƙasar Rasha ba.

erdogan, gencler1.jpg

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar Turkiyya bata fasa sayen makami ƙirar S-400 daga ƙasar Rasha ba.

Erdoğan wanda ya amsa tambayoyin matasa a lokacin ganawa da su a fadar Dolmabahçe dake lstanbul ya bayyana cewar:

"Mun kammala ciniki akan makamin S-400 , bi ma'ana babu zancen ja da baye daga sayen makamin S-400, muna alfarin kammala wannan lamari kuma zamu yi farin cikin karɓar wannan makamin a watan Yuli, ba mamaki ma mu karɓe shi da wuri, bayan kammala lamarin S-400 zamu kuma buɗe littafin S-500"

Haka kuma shugaba Erdoğan ya yi sharhi akan ko Amurka ta bayyana cewar lamurkan S400 da F-35 basu dace ba, yace babu ƙashin gaskiya akan hakan sabili da mun gudanar da dukkanin bincike.

Erdoğan ya ƙara da cewa makamin F-35 na Turkiyya dake Amurka nan bada jimawa ba Turkiyya zata karɓeta.

 

 


 

 Labarai masu alaka