"Turkiyya na tsaye daram kan kafafunta"

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya ce,wadanda ke son fakewa da rikicin Siriya don tada zaune tsaye a kasar Turkiyya su gaggauta farkawa daga barci.

1146385
"Turkiyya na tsaye daram kan kafafunta"

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya ce,wadanda ke son fakewa da rikicin Siriya don tada zaune tsaye a kasar Turkiyya su gaggauta farkawa daga barci.

Shugaban na Turkiyya ya furta wannan kalamin a wani babban taron siyasa da jam'iyyarsa ta shirya a birnin Bursan kasar,inda ya ce:

"Muna da cikakkiyar masaniya kan babbar asarar da zamu yi,idan har muka kasa tsayawa kan kafafunmu a matsalolin da suka danganci kasar Siriya.Kamar a tattalin arziki, a fannin diflomasiyya ma,dole ne mu sake zage damtse.Wadanda ke son fakewa da rikicin Sham don tada zaune tsaye a Turkiyya,su gaggauta farkawa daga barci.Hakarsu ba zata cimma ruwa ba.Kasarmu tsaye ta ke daram kan kafafunta".

Daga karshe shugaba Erdoğan,ya sanar da cewa, a taron Sochi karo na hudu wanda kasashen Rasha,Turkiyya da kuma Iran suka shirya a ranar 15 ga watan Fabrairun bana,sun aika muhimman sakwanni ga kasashen duniya ga baki daya.Labarai masu alaka