Ganyen shayin Turkiyya ya yi tasiri a idon duniya

An bayyana cewar a tsakanin watannin Janairu da Satumba Turkiyya ta fitar da ganyen shayi har na dala miliyan 8 da dubu 309 zuwa ƙasashen waje.

Ganyen shayin Turkiyya ya yi tasiri a idon duniya

An bayyana cewar a tsakanin watannin Janairu da Satumba Turkiyya ta fitar da ganyen shayi har na dala miliyan 8 da dubu 309 zuwa ƙasashen waje.

Garin Rize wacce ta sayar da ganyen shayi har na dala miliyan 258 ce ke kan gaba a fagen fitar da ganyen shayi zuwa ƙasashen waje a Turkiyya.

Shugaban kungiyar fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen ketare a gabashin Medeterranian Saffet Kalyoncu ya bayyana cewar Turkiyya ce ta biyar a fannin noman ganyen shayi a duniya.

Kalyoncu dake bayyana ganyen shayin Turkiyya a matsayin na dayɗ a nahiyar Turai ya jaddada cewa rashin sa wasu sanadaran kanfuna da ka iya cutar da bil adama da Turkiyya ba ta yi ne ya sanya karɓuwar ganyen shayin Turkiyya a idon duniya.

Kalyoncu ya kara da cewa a cikin watanni tara Turkiyya ta fitar da ganyen shayi har na ton dubu biyu da 35.

Daga cikin ganyen shayi da aka fitar har na dala miliyan 8 da dubu 309 da dari 184. Garin Rize ce kan gaba da miliyan 4 da dubu 258 da dari 443 , lstanbul kuma na binta baya da miliyan 2 da dubu 187 da dari 583 a yayinda Ankara take ta uku da dubu  697 da dari 594. Kusan rabin yawan ganyen shayin da Turkiyya ta fitar zuwa ƙasashen waje an noma su ne a garin Rize.Labarai masu alaka