An kama bakin haure 58 a Turkiyya

Jami'an tsaron teku na Turkiyya sun kama bakin haure 58 a gundumar Cesme da ke lardin Izmir.

An kama bakin haure 58 a Turkiyya

Jami'an tsaron teku na Turkiyya sun kama bakin haure 58 a gundumar Cesme da ke lardin Izmir.

Jami'in tsaron tekun su suka bazama bayan samun labarin ganin bakin hauren a gabar tekun garin Karaabdullah.

Jami'an sun tsayar da jirgin ruwan na roba inda suka ga akwai 'yan kasar Siriya 34, 'yan Iraki 20 da 'yan kasashen Yaman da Falasdin biyu-biyu.

Bayan an kammala tantance mutanen da suka hada da mata da yara kanana an mika su ga ofishin kula da 'yan gudun hijira na lardin Izmir.Labarai masu alaka