Farmakan Tafkin Zaman Lafiya

Manufar ita ce zaman lafiya,
ta'addanci ake nufa

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hürriyet na cewa, a cikin bayanin da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan yayi a yayin ziyararsa a Tanzaniya ya ce, “babban musibar dake faruwa a duniya yanzu shi ne ta’addanci, domin haka ya kamata mu hada kai wurin yaki da kungiyoyin ta’addaci. Babu ta’addar kirki ko kuma muguwa, dukkan ta’adda daya ce. Ka da ku bar mutane su yaudareku. Saboda kungiyar ta’adda ta FETÖ ce ta yi yunkurin juyin mulki a ranar 15 ga watan Yuli. Wannan kungiya ba a Turkiyya kadai ta ke ta’addanci ba, ta’addancin nasu ya isa har kasashen waje. Dukkan masoyanmu sun san cewa kungiyar na barazanartar rayuwar mutane.”

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, a yau ne karo na farko da Turkiyya da Rasha zasu gudanar da taro a Astana babban birnin kasar Kazakistan domin shawo kan matsalar rikicin da aka dauki shekaru 6 ana yi tsakanin gwamnatin Asad da ‘yan adawar kasar Siriya. Babban manufar wannan taro shi ne, ana cigaba da tsagaitar wutar da aka sanar a ranar 30 ga watan Disamba wanda kasashen Turkiyya, Rasha, Iran da wakilai daga Majalisar Dinkin Duniya da wakilan Amurka da Iran da waikilan Tarayyar Turai ke bukata. Taron dai mataimakin sakataren ma’aikatar ministan harkokin wajen Turkiyyya, Sedat Önal, da maitaimakin minsitan harkokin wajen kasar Iran da wakilai daga Amurka da kuma jakadan babban birnin Astana ne za su halarta. Bayan haka kuma, wakilin Rasha a Siriya, Alexander Lavrentiev da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rashan, Mikhail Bogdanov ne ke wakiltar shugaban Rasha Vladmir Putin a taron. A gefe guda kuma Beşar el-Caferi ke wakiltar gwamnatin Asad.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, wannan shi ne karo na farko da masu yaki da juna, wato ‘yan adawa da gwamnati suka hadu a Astana domin kawo karshen yaki da suke yi da juna. Rasha da Turkiyya ta shiga tsakanin domin ganin cewa an samu zaman lafiya a kasar Siriya domin an dade ana zubar da jini a wurin.

Babban labarin jaridar Haber Türk na cewa, ma’aikatar al’ada da yawan buda ido ta kasar Turkiyya ta fara aikin hadin gwiwa da Travel Channel. A sababin hakan za’ayi shirye-shiryen telebijan a kowacce kaka. Maimakon yin finafinan tallafa kanfanonin jama’a, Travel Channel din zaiyi hadin gwiwa da ma’aikatar Turkiyyan wajan yin finafinai masu yada kyan kasar Turkiyyan da kuma shirye shiryen telebijan a kowacce kaka.

Babban labarin Yeni Şafak na cewa, Mai kula da harkokin kasuwancin kasar waje da bada bashi na kasar Italiya, Michan Ron yace darajar hannayen jarin Italiya a Turkiyya ta kai Euro miliyan 2.8, inda ya kara da cewa, za su saka hannun jari a kasuwar na’urori da kanfanonin fasaha, da ma’aikatun kasar Turkiyyan masu kwazo amma basu da karfi.

 

 Labarai masu alaka