Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da shugaban Majalisar Tarayyar Turai Martin Schulz game da sake dokokin yaki da ta’addanci inda Erdogan ya ce, “zamu yi hakuri harzuwa karshen wannan shekara, bayan haka zamu dauki matakin da ya kamata”. Erdogan ya soki Tarayyar Turai da kakkausar murya game da taimakawa ‘yan ta’adda inda ya ce, ‘kuna taimakawa ‘yan ta’adda ta kowanne hanya, sa’anan sai ku zo ku ce ‘zaku hana Turkiyya zama mamba a Tarayyar Turai.’  Ai kun riga makara, ku dauki hukunci yanzu mana. Domin a kasar Turkiyya mutane ne ke yanke shawara. In ba haka ai nima zan iya zama yanke shawara amma sai dai ba zan yi wannan ba. Domin mutane ne zasu yanke hukunci.”

Babban labarin jaridar Habertürk na cewa, ministan harkokin waje Tarayyar Turai ya gana a Brussels game da shigar Turkiyya a Tarayyar Turai. A yayin da kasar Australia ba ta bayyana ko tana ra’ayin Turkiyya ta zama mamba ba, a gefe guda kuma, ministan harkokin wajen Ingila Boris Johnson ya bayyana cewa Turkiyya na da matukan muhimmanci inda ya kara da cewa, “bai kamata a ajje Turkiyya a gefe ba. Bai kamata mu bi da son kai da wuce kona da iri wurin daukar mataki akan wata kasa ba.” Ministocin kasashen Jamus da Faransa kuma sun sanarda cewa idan aka ki amincewa da Turkiyya ta zama mamban Tarayyar Turai a dai-dai wannan lokaci, to wannan zai iya jawo matsala.”

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, bayan yaki da aka yi da kungiyar ta’adda ta PKK, wanda suka kashe yara kanana, mata, tsofoffi, matasa da dama tare da kona gidaje, da makarantu, inda aka yi nasara akansu, a halin yanzu al’ummar Şirnak sun fara komawa a gidajensu. Da yake jami’an tsaron yankin na son a kara tsaro a yankin, a halin yanzu al’ummar Şirnak sun yi layi domin shiga cikin kasar. Wadanda suka dawo zuwa gidajensu sun yi matukan bakin ciki a yayinda suka ga yadda ‘yan ta’adda suka bata wurin. Amma a gefe guda kuma gwamnatin kasar Turkiyya ta sanar zata dauki nauyin dukkan abinda ‘yan ta’addan suka bata.

Babban labarin jaridar Star na cewa, an zabi shirin fim da ake yawan kallo a tashar TRT wato 'Diriliş: Ertuğrul’ a matsayin fim mafi kyau a taron bada lambar Altın Kelebek. Marubucin wannan shirin Mehmet Bozdağ ya yada wannan labari da murnarsa a shafinsa na Instagram. A cikin rubutun da yayi a shafinsa na Istagram, Bodağ ya ce, “masu kallonmu; da taimakonku ne aka zabi shirin fim din 'Diriliş: Ertuğrul’ a matsayin fim mafi kyau a taron bada lambar yabon Altın Kelebek na karo 43. An dauki tsawon makonni 65 ana nuna wadan fim a cikin akwatunan talebijin a kasar Turkiyya tare da kasashe 30 kuma ana ci gaba da yabawa aikin da muke yi. Imba don ku ba, da bamu san yadda zamu yi ba. Ina matukan godiya gareku.”Labarai masu alaka