An kama mambobin Daesh ‘yan kasashen waje 40 a Istanbul

Jami’an tsaro a Istanbul sun kai farmaki kan mambobin kungiyar ta’adda ta Daesh inda aka kama muatne 40 ‘yan kasar waje.

572587
An kama mambobin Daesh ‘yan kasashen waje 40 a Istanbul

Jami’an tsaro a Istanbul sun kai farmaki kan mambobin kungiyar ta’adda ta Daesh inda aka kama muatne 40 ‘yan kasar waje.

Sashen Yaki da Ta’addanci da Nemo Bayanan Sirri na helkwatar ‘yan sandan Istanbul da kuma jami’an gundumar Fatih ne suka fara kai farmakai kan ‘yan ta’addar Daesh a gundumar.

Jami’an sun gano adreshin gidajen da ‘yan kasar waje mambobin kungiyar suke zama.

A farmakan da suka kai a gidaje 23 da ‘yan ta’addar suke sun kama mutane 40 da suka fito daga kasashen Azabaijan, Iran, Iraki da Afganistan.

An kuma kwace kayan aiki da takardu a binciken da aka gudanar a gidajen.

An bayyana cewa, da yawa daga cikin wadanda aka kama din sun taba zuwa yankunan da ake rikici a kasar Siriya.

 Labarai masu alaka