Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin Haberturk na cewa, bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a ranar 15 ga watan Yuli a kasar Turkiyya, shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ya fitarwa masu zuba jarin kasashen waje sako. Erdogan ya ce, "shekaru 14 kenan babu wanda yayi asarar dukiya a cikin wadanda suke zuba jari a kasar Turkiyya, sai dai samu da suka yi. Kuma zasu ci gaba da samun riba a kasar Turkiyya. Domin ba zamu yarda mu zauna muna kallo masu zuba jarin kasashen waje su shiga cikin matsala a kasar Turkiyyya ba."

Babban labarin jaridar Star na cewa, ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya gana da wani jaridar kasar Jamus Frankfurter Allgemeine Zeitung (FAZ) inda yayi bayani game da yunkurin juyin mulkin da kungiyar ta'adda ta FETO ta yi a ranar 15 ga watan Yuli. Bayan bayanin da yayi cewa 'idan ba a rike alkawarin viza ba, yarjejeniyar zata ba ce', sai Tarayyar Turai suka rikice. A lokacin da ministan harkokin wajen kasar Australia Sebastian Kurz ya fitar wata sako a shafinsa ta Twitter cewa, 'ba zan amince da abubawanda wani ke so ba, kamata ne ayi aiki da dokokin da Tarayyar ta tanada', sai takwararsa Cavusoglu kuma ya maida masa martani da cewa 'ba lalle ina cewa sai an amince da bukata ta ba, ni kawai ina bada ra'ayi na ne.'

Babban labarin Yeni Şafak na cewa fitar da kaya da Turkiyya ke yi ga kasashen waje ya sauka da kaso 32.2 cikin dari a watan Yuli inda ya kama dalar Amurka miliyan 4.78. A cikin farkon watanni 7 na shekarar 2016 an samu ci gaba a bangaren fitar kaya zuwa kasashen waje da kaso 71.3. Ministan tattalin arzikin kasar Turkiyya Nihat Zeybekci ya fitar da wata sanarwa ta shafinsa ta Twitter inda y ce, idan aka hada da kasuwancin jaka da kananan kasuwanci da ake yi a yankunan kasashen Turkiyya, za a samu ci gaba fin haka. Shi ya sa an samu ci gaba sosai a bangaren fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje."

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, filin EXPO 2016 da aka bude a Antalya na ci gaba da karbar bakuncin shahararrun mutanen kasashen duniya. Farkon bakon da zai ziyarci Antalya a cikin watan Agusta shi ne shahararren mawakin nan Sting wanda ya taso ya shahara tun daga shekarar 1989 kuma ya samu lambar yabon Grammy har sau 10. Tun daga lokacin da ya fara aiki har zuwa yau, an sayar da album din wake-wakensa kusan miliyan 100. Yana cikin mawakan da suka cashe kuma suka samu lambar yabon Emmy da Tony. Bayan ziyarar Sting zuwa EXPO da mako daya, Enrique Iglesias zai kawo ziyara a wurin. Labarai masu alaka