Ana taron nasarar yakin Istanbul

Mutane da dama sun hadu suka yi sallar asuba a masallacin Aghia Sophia domin tunawa da nasar yakin Istanbul.

499238
Ana taron nasarar yakin Istanbul

Mutane da dama sun hadu suka yi sallar asuba a masallacin Aghia Sophia domin tunawa da nasar yakin Istanbul.

Asusun matasan kasar Turkiyya da kungiyar matasan yankin Anatolia ne suka hada wannan taro inda mutane da dama suka hadu a dandanlin Aghia Sophia domin su yi sallar asuba.

Shugaban asusun matasan kasar Turkiyya Salih Turhan ya ce, masallacin Aghia Sophia yana da matukan muhimmanci a duniyar musulmai inda ya kara da cewa wannan shi ne dalilin da ya sa suka hadu a wurin domin su yi sallar asuba.

Mutane da dama a wurin taron sun bayyana cewa, masallacin Aghia Sophia wani alama ce na birnin Istanbul, domin da aka bukaci Fatih Sultan Mehmet ya maida wurin a matsayin wurin ibada, sai yayi hakan ba tare da jinkiri ba.Labarai masu alaka