Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya.

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hürriyet na cewa, babban sakataren NATO Jens Stoltenberg ya amsawa jaridar Hürriyet wasu tamboyoyi bayan ya gana da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan tare da firaministan Ahmet Davutoğu da kuma ministan harkokin waje Mevlüt Çavuşoğlu a ziyarar da ya kai a babban birnin Ankara. A cikin jawabin da yayi ya ja hankalin mutane game da hana anfani da sararin samaniya Siriya da aka yi inda ya ce "NATO bata cikin wannan al'amarin". Stoltenberg ya bayyana cewa, zasu kara taimakawa Turkiyya a iyakar da ake tashin hankali musammanma a Kilis.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, a wannan shekarar yara 125 daga kasashe 12 ne suka zo kasar Turkiyya domin halartar bikin yara ta 23 ga watan Afrilu. Da farko yaran sun hadu a birnin Istanbul inda suka nuna kayayyakin gargajiya da suka fito da shi daga kasashensu inda suka yi burodin zaman lafiya da alkama da kowa ya tawo da shi. Wannan burodin zaman lafiya da suka, za a aika wa manyan shugabanin kasashen duniya kamar shugaban Amrika Barack Obama da Firaministan gwamnatin Jamus Angela Merkel​.

Babban labarin jaridar Haberturk na cewa International Council of Shopping Centers (ICSC) ta zabi Mall of Istanbul a babban wurin sayayya na nahiyar Turai. Mall of İstanbul ta karbi wannan kyauta ne a taron da aka gudanar a Milano. Shekaru biyu kenan da aka bude Mall of İstanbul wanda ke dauke da ma'aikata dubu 6 da 500 tare masu ziyarar wurin kusan miliyan 30. Wannan wuri na jan hankalin 'yan yawon bude ido kuma tana nuna muhimmancin al'adu da sana'a a cikin rayuwar mutane. ​

Babban labarin jaridar Sabah na cewa shirin EXPO na shekarar 2016 da za a gudanar da Antalya a babban filin shakatawa na yara da ke da fureni zai taimaka wurin tallata birnin Antalya da ci gabanta. Wannan taron da zai dauki tsawon watanni 6, shahararrun mawakan zamani da na gargajiya zasu halarci. Za a bude taron ne da wakan Maroon 5​ bayan haka kuma mawaka kamar Deep Purple, Scorpions, Muse, Sting, Sean Paul, Simply Red, Jose Carreras, UB40, Status Quo​ zasu zo su cashe. Bayan haka kuma Dj David Gueta​ ne zai cashe a bikin rufe taron.Labarai masu alaka