Birnin Istanbul (3)

Idan mutum na da ikon ya kalli duniya sau daya, to wannan mutumin ya kamata ya kalli Istanbul. Akwai manyan malamai, sana’o’i da yanayi mai ban sha’awa wadannan su ne suka hadu suka sanya birnin Istanbul ya zama mai muhimmaci.

Birnin Istanbul (3)

Shahararren mawakin nan dan kasar Faransa, marubuci kuma dan siyasa Alphonse Lamartine, ya yi bayani game da birnin Istanbul saboda ya zagaya daga nahiyar Asiya zuwa nahiyar Turai inda ya koyi al’adu da dama a bangarori daban-daban.

Masu sauraron mu barkanmu da warhaka. A cikin littattafan soyayya da Lamartine ya rubuta game da Istanbul a shekarar dubu biyu da goma yana tunatar da mutanen Turai da Asiya game da wannan birni.

A yau yawan mutane dake rayuwa a Istanbul sun kai miliyan dubu goma sha biyu, inda girmansa ya kai kilomita dubu biyar da dari bakwa da goma sha daya har akan ce girmansa ya fi biranen kasashen Turai da dama... Bayan da aka zabi Istanbul a matsayin babban birnin al’ada na kasashen Turai a shekarar dubu biyu da goma, an yi ayyukka da taruka da dama a birnin. Yau za mu ambaci wasu aikace-aikace da dama da ake yi a birnin. Bayan an kammala aiyukan, Istanbul zai jawo hankulan mutanen duniya baki daya.

Mun bayyana a cikin shirye-shiryenmu cewa.” Istanbul ya zama babban birni na al’adun Turai a shekarar dubu biyu da goma” kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin gwamnati ne suka shirya taron. Wadannan mutane sun fara wani aiki domin sun gyara birnin Istanbul. Da farko kungiyoyin sun fara gyara babbar cibiyar al’ada mafi muhimmaci dake Istanbul mai suna “Atatürk Kültür Merkezi”. Mun fada muku wannan ne saboda yana da muhimmmaci. Dandalin Taksim na cikin dandali mai muhimmaci da ake kalubale game da shi a birnin Istanbul. A wannan dandali na cibiyar al’adun Istanbul, ana wasan kwaikwayo, kide-kide da wake-wake kuma a wurin ne ake tarukan raya al’adu da dama.

Wannan shi yasa ofishin ministan al’adu da kungiyar dillalan raya al’adu na shekarar dubu biyu da goma suka dauki mataki akan cewa za su gyara wurin. An dauki matakin cewa za’a gyara wurin ne a lokacin da aka zabi Istanbul a shekarar dubu biyu da goma. Wannan gini ya kara kayayyakin al’adu da dama kuma za’a bude dakunan zane-zane a tsakiya. Wannan aikin gyara cibiyar al’adu ta Ataturk, babban birni na al’ada na kasashen Turai Istanbul ne ke yi. Za su gyara cibiyar ne don gabatar da wake-wake zuwa kide-kide, saboda ci gaba da al’adu. Za’a tsara wannan cibiyar al’adu ne domin yadda za ta jawo hankalin mutane a wurin kuma za’a saka wutar lantarki saboda yadda ba za’a sami matsala ba. Saboda haka, wannan cibiyar al’adu za’a a bude ta kwana dari uku da sittin da biyar dare da rana. Ma’ana koyaushe a bude take.

Kamar yadda muka ambata da farko, za’a saka wutar lantarki, tsaro, wurin gyara sauti da wasu abubuwa da dama. Wannan wuri an gina shi a shekaru da dama da suka wuce kuma ba’a samu wanda zai gyara ba, shi ya sa wannan kungiyar ta raya al’adu suka dauki mataki akan cewa za su gyara.

Jama’a masu sararonmu, shin kun san wani abu? Shin kun san a duniya menene babban abu da kuma shahararen abin da ke jan hankalin mutane zuwa kasashen China da Japan?

Ba tare da bata lokaci ba za mu bayyana muku dalili. Kayyakin ado da kasashen China da Japan suke amfani da su su ke jawo hankalin mutanen duniya su yi koyi daga fadar Topkapı dake babban birnin Istanbul. An gina fadar Topkapı ne a shekarar dubu daya da dari hudu da saba’in da takwas miladiyya, bayan Fatih Sultan Mehmet ya jagoranci yakin karbar Istanbul, bayan shekara dari uku da tamanin sai aka kuma gina fadar Dolmabahce a karkashin jagorancin Sultan Abdulmajid inda aka mai da wurare biyun a matsayin majalisar Daular Usmaniyya.

Fadar Topkapı da Dolmabahce su ne fada biyu da har yanzu ake gyaran ciki tun lokacin Daular Usmaniyya da ake gyarawa lokaci zuwa lokaci. Shahararren abu daga cikin fadar shi ne dakin girki. Shahararren mai gini Mimar Sinan ne ya gina wannan dakin girki; wurin yana daukan masu yin abinci guda dubu daya da dari biyu da kullum suke girgi kuma a yau idan ka je kasashen China da Japan, za ka samu irin abincin da suke yi a lokacin. A lokacin kayayyakin abinci dubu goma sha biyu ne suke amfani da shi, amma a yau sauran dubu biyu da dari biyar.

Idan ka duba yanayin lokacin, zaka ga cewa abinda Sultan ke tsoro shi ne a saka guba a cikin abinci domin a kashe wani. Saboda Sultan na tsoron hakan ne ya sa kowanne lokaci sai an wanke kwanon abinci sannan su fara cin abincin.

Domin a samu a nuna wadannnan kayayyakin abincin fadar China da Japan a fadar Topkapı ne kungiyar raya al’adun manya kasashen Turai a shekarar dubu biyu da goma ne suka gyara fadar. Bayan an gama gyara wannan fadar mutanen Istanbul da duniya baki daya sun ga tsantsar kaye na al’adu da dama a wurin. Ta haka ne mutane suka gane asalin kayan al’adun babban birnin Istabul. Dukkan wadannan aiyuka ana yi domi kare kayayyakin al’adun wurin.

Ba wurin tarihi guda biyun kadai aka gyara a garin ba. A cikin aikin kungiyar da ta yi a babban birnin al’adu Istanbul, an gyara ofishin shugaban kungiyar inda za’a sake gyaran wuraren tarihi guda tamanin da takwas. A cikin wannan wurare, akwai masallacin Sulaimaniye wanda aka gina shi shekaru dari hudu da suka gabata. Sannan, an gyara masallatai kamar, Nuruosmaniye mai taga 171, masallacin Valide Sultan, masallacin Fatih, da kuma masallacin Yavuz Sultan Salim. An gyggyara su. Kuma ana gyara kasuwar Masar dake Istanbul.

A yanzu ana shirye-shiryen gyara wuraren tarihi da dama a birnin na Istanbul. A mako mai zuwa za mu ci gaba da baku labarin shirin gyare-gyaren wuraren tarihi. idan an kammala gyare-gyaren wuraren tarihin, birnin Istanbul zai zama inda ke dauke da wurin tarihi da yafi ko’ina a duniya baki daya.

Sai an jima daga Muryar Turkiyya.


Tag:

Labarai masu alaka