Ana ci gaba da sayar da tikitin zuwa yawon bude ido duniyar sama

Shugaban Kamfanin Amazon Jeff Bezos ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu kamfaninsa na Blue Origin ya sayar da tikiti na dala miliyan 100 ga masu sha'awar zuwa duniyar sama yawon bude ido.

1678179

Bezos ya gudanar da taron manema labarai bayan ya dawo daga yawon bude ido a duniyar sama inda ya godewa ma'aikatan Amazon da abokan huldarsu bisa daukar nauyin tafiyar tasa.

Ya shaida cewa, sun samu bukata daga mutane sama da yadda suka yi tsammani, kuma tafiyar ta yi dadi da kayatarwa.

Bezos ya kuma ce, kamfanin Blue Origin ya karbi bukata da yawa daga jama'a, kuma ya zuwa yanzu sun sayar da tikiti na dalar Amurka miliyan 100.

Bezos bai bayyana nawa ake sayar da tikicin ba, amma ya ce a wannan shekarar Blue Origin na son gudanar da balaguro zuwa duniyar sama har sau 2.

Biloniyan dan kasar Amurka tare da wasu mutane 3 sun yi nasarar zaga duniyar sama a cikin kumbon New Shepard da kamfaninsa na Blue Origin ya samar.Labarai masu alaka