Amurka za ta baiwa Rasha kyautar na'urorin taya numfashi

Ministan Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewar a karkashin yaki da annobar Corona (Covid-19), za su baiwa Rasha kyauta na'urorin taya numfashi guda 200.

1420959

Pompeo ya fitar da sanarwa ta shafin Twitter game da taimakon da Amurka ke bayarwa wajen yaki da annobar Corona a duniya.

Pompeo ya ce Amurka ta zama shugaba wajen bayar da tallafin yaki da corona a duniya, sun shirya aika na'urorin taya numfashi dubu 15 zuwa ga kasashen duniya 60.

Pompeo ya ci gaba da cewar suna ba wa Rasha taimako kuma Amurka za ta aika mata da na'urorin taya numfashi guda 200.

A watan da ya gabata Rasha ta aike da kayan taimakon yaki da Corona ga Amurka a cikin jirgin soji na dakon kaya samfurin AN-124.

Kakakin Fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya gode wa rasha a lokacinda kayan suka isa gare su.Labarai masu alaka