Corona: Giya mara inganci ta yi ajalin mutane 320 a Iran

Mutane 320 sun rasa rayukansu a Iran sakamakon shan giya mai guba bayan samun labarin cewar tana hana kamuwa da cutar Corona (Covid-19).

1389175
Corona: Giya mara inganci ta yi ajalin mutane 320 a Iran

Mutane 320 sun rasa rayukansu a Iran sakamakon shan giya mai guba bayan samun labarin cewar tana hana kamuwa da cutar Corona (Covid-19).

Kamfanin dillancin labarai na Fars dake Iran ya rawaito kakakin ma'aikatar Lafiya ta kasar Kiyanush Cihanpur na cewa daga 6 ga watan Maris zuwa yau mutane dubu 3,117 ne suka je asibiti sakamakon shan gurbatacciyar giyar da ta illata su da sunan neman kariya daga cutar Corona.

Cihanpur ya ce daga cikinsu mutane 320 sun rasa rayukansu, wasu 62 kuma sun rasa ganinsu baki daya.

Kakakin ya ci gaba da cewar ana kula da mutane dubu 1,066 a asibiti wadanda 73 daga ciki na dakin kula da wadanda ke cikin mawuyacin hali.

An kama mutane da dama dake samar da giya gurbatacciya a Iran.

Labarai masu alaka