Yukren ta yi gwajin jiragen yaki marasa matuki da ta saya daga Turkiyya

Yukren ta yi gwajin jiragen yaki marasa matuki samfurin Bayraktar TB2 da ta saya daga wajen Turkiyya.

1378729
Yukren ta yi gwajin jiragen yaki marasa matuki da ta saya daga Turkiyya

Yukren ta yi gwajin jiragen yaki marasa matuki samfurin Bayraktar TB2 da ta saya daga wajen Turkiyya.

Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Tsaro ta Yukren ta fitar ta ce, sojojin Yukren sun fara amfani da jiragen yaki marasa matuka na Bayraktar TB2.

Sanarwar ta ce "Tuni aka yi gwajin jiragen tare da bayar da horon yaki da su."

Sanarwar ta kara da cewar jiragen Bayraktar TB2 za ta kara karfi ga rundunar sojin Yukren, kuma hare-haren da aka kai wa sojojin Asad a Siriya da jiragen ya tabbatar da irin karfin da suke da shi.

Yukren ta sayi jiragen yaki marasa matuki samfurin Bayraktar TB2 guda 6 daga wajen Turkiyya kuma ta samu nasarar gwada amfani da su.Labarai masu alaka