OPEC ta yanke shawarar rage fitar da man fetur

A taron kungiyar kasashe masu arzikin man fetur a duniya OPEC dake gudana a birnin Biyana ne dai aka yanke shawarar cewa za a rage fitar da man fetur mai yawan ganda dubu 500 a kullun.

OPEC ta yanke shawarar rage fitar da man fetur

A taron kungiyar kasashe masu arzikin man fetur a duniya OPEC dake gudana a birnin Biyana ne dai aka yanke shawarar cewa za a rage fitar da man fetur mai yawan ganga dubu 500 a kullun. 

An zartar da al'amarin ne a taron ministoci da ake gudanar wa a karo na 7 karkashin Kungiyar OPEC a Biyana babban birnin Ostiriya. 

A watan Satumban shekarar 2018 ma dai an yanke shawarar rage ganga miliyan 1.2 a kullum inda yanzu kuma aka kara dubu 500 akan adadin inda za a cigaba da amfani da dokar har zuwa watan Maris shekarar 2020. 

Ministan Harkokin Makamashin Kasar Saudiyya Abdulaziz bin Salman ya bayyana cewa Saudiyya ce za ta rage ganga dubu 167 cikin ganga dubu 500 da aka yanke shawarar za'a rage.

Haka zalika ministan ya ce Saudiyya za ta rage ganga dubu 400 da kanta ba tare da tilastawar kungiyar ba. 

 

 


Tag: Saudiyya , OPEC

Labarai masu alaka