An samu ribar fitar da kayayyaki daga Turkiiya har dala biliyan 164

Ministar Kasuwanci ta Turkiyya, Ruhsar Pekcan ta sanar cewa fitar da kayayyaki daga kasar a Nuwamba ya samar da riba dala biliyan 164 da miliyan 214.

Ruhsar Pekcan ta ba da sanarwar fitar da kayayyakin watan Nuwamba a Istanbul. Pekcan ta ce 'Duba da habaka da aka samu a wattani 3 na ukun wannan shekaran za a iya cewa mun samu ci gaba kuma za a ga alkaluma mafiya kyau a karshen shekara.' 

Ministar Kasuwanci Pekcan, ta ce "A fitar da kayayyaki a watan Nuwamba an samu riba dala biliyan 164 da milyan 214. Wannan shi ne adadi mafi girma na 4 da muka taba samu a wata 1." 

Ta kara da ce wa "Fitar da kaya zuwa kasashen waje ya karu da kaso 1.77 cikin 100 a watanni 11 idan aka kwatanta da wannan lokacin na shekarar da ta gabata inda ya kai dala biliyan 165 da miliyan 675 da kuma ya ci gaba da tafiya mai kyau. "Adadin fitar da kayayyaki zuwa shigo da kayayyaki a bara ya kasance kashi 75.6 cikin 100 ne yanzu kuma ya karu zuwa kashi 86.8 cikin 100." 

 Labarai masu alaka