'Ya'yan kashu sun yi badago a hannun manoma a Yammacin Afirka

A kasashen Yammacin Afirka da suka hada da Sanagal da Ivory Coast 'ya'yan Kashu ko yazawa sun kasance a hannun manomansu.

'Ya'yan kashu sun yi badago a hannun manoma a Yammacin Afirka

A kasashen Yammacin Afirka da suka hada da Sanagal da Ivory Coast 'ya'yan Kashu ko yazawa sun kasance a hannun manomansu.

Mafi yawan kashu ana noma shi a kasashen Benin, Sanagal, Ivory Coast, Najeriya da Gini-Bissau, kuma a yanzu manoman sun gaza samun masu saya da daraja.

'Ya'yan kashu din da a baya ake sayar da kilo daya kan saifa 375 a Ivory Coast da ta fi kowacce kasa samar da shi, amma a yanzu a kan saifa 50 ma an rasa wanda zai saya.

Kwararru sun bayyana cewar babban abinda ya janyo wannan abu shi ne yadda masu sayen kashu daga Asiya suka ajje wanda suke da shi a rumbunansu a shekarar da ta gabata saboda tsada da ya yi, kuma ba za su sayi sabo ba sai sun karar da wanda yake hannunsu.

Kwararrun na cewar wannan matsala ba za ta dauki dogon lokaci ba.Labarai masu alaka