Babbar Bushara ga 'yan Najeriya daga gwamnatin Buhari

Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama na Najeriya Sanata Hadi Sirika ya bayyana cewa, a karshen wanna shekarar ake sa ran kaddamar da wasu daga cikin jiragen saman Najeriya da za su dinga aikin diban fasinjoji.

Mista Sirika wanda tsohon matukin jirgin sama ne ya bayyana hakan a öokacin da ya ke karbar takardun tabbatar da fara aikin jiragen da mallakarsu daga Darakatan da ke kula da shirin Chidi Izuwah.

Sirika ya ce, gabatar da takardun shaida ne kan yadda aiyukan suke tafiya.

Kamfanin Jiraagen Saman da zai fara aiki zai lashe dala miliyan 8 da kuma dala miliyan 300 na fara aiyukansa.

Ministan ya kara da cewa, ba gwamnatin Najeriya ce za ta dauki nauyin dukkan aiyukan samar da jiragen, za a yi hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zba jari a aikin.

Ya ce, a watan Disamba Najeriya za ta karbi jiragen sama 5 a karkashin shrin wanda za su fara aikin diban fasinjoji.

'Yan Najeriya dai tsawon shekaru 3 na ci gaba da jiran sharbar romon demokradiyya daga gwamnatin Buhari wadda har yanzu bayan shekaru 3 ta ke ci gaba da yin alkawururruka ga 'yan kasar tare da cewa, tana kokarin gyara barnar da aka yi a baya.

 Labarai masu alaka