Taron kolin NATO da dangantakar Turkiyya da Amurka

Tattaunawar Erdogan da Biden ta kasance mai muhinmanci kwarai da gaske tamkar yadda aka saba,  kuma za ta kasance ma'aunin awna lamurra da dama a 'yan shekarun dake tafe

1661515
Taron kolin NATO da dangantakar Turkiyya da Amurka

Babban lamarin da ake tattaunawa akai dangane da taron kolin Kungiyar NATO a Brussels shi ne dangantakar Turkiyya da Amurka.

A wannan makon ma akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da Ferfesa Murat Yeiltas Daraktan Harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa,  Tattalin arziki da Hallayar dan Adam wato SETA..

Tattaunawar Erdogan da Biden ta kasance mai muhinmanci kwarai da gaske tamkar yadda aka saba,  kuma za ta kasance ma'aunin awna lamurra da dama a 'yan shekarun dake tafe. Turkiyya ta bayyana dabi'u guda uku wadanda ke bayyana huldarta da wata kasa. Daya daga cikinsu shi ne bayyana cewa akwai dangantaka tsakaninsu da wata kasar da kuma sake gina dangantakar. Bayan yakin cacar baki, kasashen biyu sun bayyana irin hulda dake tsakaninsu ta yin amfani da kalmomi da dama. A siffar hulda tsakaninsu ko wace kasar ta yi amfani da kalmomi bisa tsariq mai kima da ingattaciyar dangantaka wadanda zasu iya kasancewa ko kuma su kasance na baka kawai. Hakan ya sanya hulda tsakaninsu ba ta yi wata babban tasiri ba. Hakan ya kuma sanya Turkiyya neman ayyanar da huldar da za ta mutunta 'yancinta wacce kuma za ta kasance bisa daidaito.

Ďabi'a ta biyu kuwa ita ce ayyanar da hulda wacce ta dace. Turkiyya ta tunatar da cewa hulda ta nesa da nesa ba ta haifar da wani dan mai ido ba tsakanin kasashen biyu. A hakikanin gaskiya hulda ta nisa da nisa tsakanin Ankara da Washington bisa kawancen Amurkawa da Turkawa bai kasance abinda ake bukata ba. Bayanan da Biden ya yi ya nuna cewa yana bukatar a samar da mafita ga matsalolin da kasarsa keda su da Turkiyya.

Babban kalubalen dake fuskantar dangantakar dake tsakanin Turkiyya da Amurka shi ne rashin fahimtar juna ko kuma ace fahimtar juna bisa kuskure. A tattaunawar Erdogan-Biden an tabo batutuwan PYD-YPG, FETO, S-400 da sauran lamurra da dama. A gefe guda kuma, ba'a yi watsi da lamarin kakkabawa ma'aikatar tsaron Turkiyya takunkumin CAATSA da Amurka ta yi sabili da siyar wasu makamai daga Rasha ba. Dukkan shugabanin biyu sun yi nuni da cewa ma'aikatun bangarorin biyu da lamarin ya shafa zasu tattauna da juna. A sabili da haka ana sa ran za'a rage kaifin wasu matsaloli a yan kwanakin dake tafe.

A ganawar, wani lamarin da aka kuma baiwa muhinmanci shi ne cigaban huldar Turkiyya-Amurka. Bayanan da aka ji bayan tattaunawar na nuni da cewa dangantaka tsakanin kasashen biyu zai ci gaba da gwabi.

Idan Turkiyya da Amurka zasu iya cimma matsaya kan wadannan ka'idoji guda uku, to zai yiwu a tattaunawa game da wasu batutuwan dake tsakaninsu yadda ya kamata. Duk wata tsarin da ta yi biris da irin bunkasar da Turkiyya ke yi da kuma tasirin da take dashi a matakin kasa da kasa ko shakka babu ba zai yi nasara ba. Ana dai ganin Amurka ta fahimci hakan. Hakan na nuni da bude sabon shafi da samar da wata dama ga dangantakar Turkiyya da Amurka.  

Wannan sharhin Ferfesa Murat Yeiltas ne Daraktan Harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa,  Tattalin arziki da Hallayar dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya,  ku huta lafiya...Labarai masu alaka