Amurka za ta tura karin sojojin kasa zuwa Afganistan

Amurka za ta tura karin sojojin kasa zuwa Afganistan domin kara karfafa tsaro.

1635280
Amurka za ta tura karin sojojin kasa zuwa Afganistan

Amurka za ta tura karin sojojin kasa zuwa Afganistan domin kara karfafa tsaro.

Kakakin Ma'aikatar Tsaro ta Amurka Pentagon John Kirby ya shaida cewa, a lokacin da Amurka ke janyewa daga Afganistan, suna shirin kara tura sojojin kasa don karfafa tsaro a kasar.

Kirby ya kara da cewa, sun kara yawan jiragen yaki masu jefa bam samfurin B-52 zuwa 6.

Ya ce, a baya kwai jiragen guda 4 a kasar.

Kirby ya kuma ce, za su ci gaba da daukar matakan tabbatar da tsaro a lokacin da dakarunsu suke janyewa daga Afganistan.Labarai masu alaka