Cavusoglu ya aike da sakon ta'aziyya ga Chadi

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fitar da sakon ta'aziyyar mutuwar Shugaban Kasar Chadi Idris Deby wanda ya rasu a fagen daga a lokacin da yake fafata rikici da 'yan tawaye a arewacin kasar a karshen makon nan.

1625272
Cavusoglu ya aike da sakon ta'aziyya ga Chadi

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fitar da sakon ta'aziyyar mutuwar Shugaban Kasar Chadi Idris Deby a fagen daga a lokacin da yake fafata rikici da 'yan tawaye a arewacin kasar a karshen makon nan.

A sakon da Cavusoglu ya fitar ta shafin Twitter ya ce, sun yi bakin ciki da samun labarin mutuwar Idris Deby Itno a fagen daga.

Ya ce, "Muna sukar hare-haren da ake kaiwa Chadi. Ina Addu'ar jin kan Allah ga Marigayi, ina kuma mika sakon ta'aziyya ga gwamnati da jama'ar Chadi.

A jawabin da Kakakin Rundunar Sojin Chadi Janaral Mermandoa Agouna ya fitar ta kafar talabijin din kasar ya bayyana cewa, Shugaba Itno mai shekaru 68 ya ransa bayan raunukan da ya samu a yayin fafata rikici da 'yan tawaye a arewacin kasar.

 Labarai masu alaka