Mataimakin shugaban kasar Turkiyya ya halarci rantsar da sabon shugaban kasar Nijer

Mataimakin shugaban kasar Turkiyya Fuat Oktay ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum

1614047
Mataimakin shugaban kasar Turkiyya ya halarci rantsar da sabon shugaban kasar Nijer

Mataimakin shugaban kasar Turkiyya Fuat Oktay ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum.

Oktay ya gana da sabon shugaban kasar jin kadan bayan rantsar dashi inda suka tattauna akan bude sabon shafin dangantaka tsakanin Turkiyya da Nijer.

Daga bisani kuma Oktay ya gana da mataimakin shugaban Sudan Mohammed Hamdan Dagalo daga bisani kuma ya gana da shugaban majalisar kolin Libiya Halid El-Meshri.

Oktay, ya mika sakon fatan samun nasara a mulkinsa daga al'umman Turkawa da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

 Labarai masu alaka