Pakistan ta harbo jirgin saman Indiya

Dakarun sojin Pakistan sun harbo wani jirgin saman soji mara matuki na Indiya a yankin LoC da ke tsakanin kasashen 2 sakamakon karya ka'idar amfani da sararin samaniyarta da ya yi.

1445043

Kakakin Rundunar Sojin Pakistan Manjo Janar Babar Iftikhar ya fitar da sanarwa ta shafin Twitter cewar, jirgin na Indiya ya karya ka'idar amfani da sararin samaniyar Pakistan a nisan kilomita 850.

Janar Iftikhar ya kara da cewar dakarun sojin Pakistan ne sua harbo jirgin na Indiya mara matuki, kuma shi ne irin sa na 9 da suka harbo mallakar Indiya a wannan shekarar.Labarai masu alaka